Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da sauya sunan Federal University of Science and Technology, Azare zuwa Sheikh Dahiru Usman Bauchi University of Science and Technology.
Shugaban Ƙasar ya bayyana hakan ne yayin wata ziyarar ta’aziyya da ya kai wa iyalan marigayi fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, a Jihar Bauchi da ke Arewa maso Gabashin Najeriya.

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, tare da manyan jami’an gwamnati ciki har da Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, gwamnonin APC, ministoci da sauran manyan jami’ai, ya kai ziyarar ta’aziyya Bauchi karon farko tun bayan rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi.
Shugaban Ƙasar, wanda bai samu halartar jana’izar ba, ya wakilci kansa ta hannun Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, makonni biyu da suka gabata.
Sai dai a wannan karo, Shugaba Tinubu ya isa Jihar Bauchi domin nuna tausayawa da jajantawa ga iyalan marigayin da kansa.
Shugaban Ƙasar ya bayyana marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi a matsayin mutum mai gaskiya, riƙon amana da kyakkyawan ɗabi’a, tare da jaddada cewa rayuwarsa da koyarwarsa abin koyi ne ga al’umma. Ya kuma ce Sheikh Dahiru Usman Bauchi jajirtaccen ɗan ƙasa ne da ya bayar da gagarumar gudummawa wajen haɗin kan ƙasa da ci gabanta.
Domin girmama irin gudummawar da marigayi Sheikh ya bayar, musamman a fannin ilimi da yaɗa ilimin addinin Musulunci, Shugaban Ƙasar ya amince da sauya sunan Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Tarayya da ke Azare zuwa sunansa.

Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, tare da ɗan marigayin, Bashir Dahiru, sun yabawa Shugaba Tinubu bisa kulawa da tausayi da ya nuna wa iyalan marigayin da al’ummar Jihar Bauchi, inda suka bayyana ziyarar a matsayin abin godiya da farin ciki ga daukacin jihar.

An gudanar da addu’o’i na musamman da karatun Alƙur’ani domin neman rahamar Allah ga ran marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi.



