Sunday, April 19, 2026
36.1 C
Bauchi

SEMA Ta Rabawa Mutanen Bauchi Tallafin Iftila’i

By Amina Umar

Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Bauchi (SEMA) ta gudanar da wani muhimmin shirin rarraba tallafin iftila’i ga mutanen da suka gamu da bala’i a Yankari Express Co-optation, cikin karamar hukumar Bauchi. Rarraba taimakon ya gudana ne a yau Talata, 5 ga Nuwamba, 2025, tare da halartar jami’an gwamnati da masu cin gajiya.

Shugaban karamar hukumar Bauchi, Hon. Mahmood Babamaji, shi ne ya jagoranci aikin rarraba kayan tare da hadin guiwar jami’an SEMA. Ya ce manufar shirin ita ce tallafa wa mutanen da suka yi asara sakamakon ambaliyar ruwa, gobara da sauran iftila’i da suka shafi yankin.

A cewar Hon. Babamaji, gwamnatin Jihar Bauchi karkashin jagorancin Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed tana daukar matakai na musamman wajen rage radadin da jama’a ke fuskanta. Ya bayyana cewa irin waɗannan shirye-shirye alama ce ta gwamnati mai karɓar kuka da taimakon jama’a ba tare da wariya ba.

Shugaban ya kuma tabbatar da cewa za a ci gaba da gudanar da rarraba irin wannan tallafi a sauran unguwanni da yankuna da lamarin ya shafa. Ya kara da cewa gwamnatin karamar hukumar Bauchi na tare da SEMA wajen tallafawa duk inda akai samun matsalar iftila’i.

Wasu daga cikin wadanda suka amfana sun nuna farin cikinsu tare da yabawa gwamnatin jihar bisa wannan kulawa da ta nuna. Sun ce tallafin ya zo a daidai lokacin da suka fi bukata, domin zai taimaka musu wajen farfado da rayuwarsu da sake farawa daga inda bala’in ya daburce su.

Wani daga cikin masu cin gajiyar tallafin ya ce sun jima suna jiran irin wannan taimako domin asarar da suka yi ta yi yawa. Ya yi godiya ga gwamnatin jihar da hukumar SEMA, yana fatan irin wannan kulawa za ta ci gaba.

Jama’ar yankin sun yi addu’ar Allah ya ba gwamnati ikon ci gaba da gudanar da ayyukan jin kai, tare da kara nutsuwar shugabanni domin taimakon al’umma. Sun ce ci gaba da kawo irin wannan taimako zai kara dankon zumunci tsakanin gwamnati da talakawa.

Related Articles

Popular Categories