Hukumar Tsaro ta Kasa, wato DSS, ta sallami sama da ma’aikatanta 100 a wani yunkuri na ci gaba da gyaran cikin gida.
Rahotanni sun bayyana cewa, jami’ai 115 ne abin ya shafa, inda hukumar ta ce matakin ya zama dole domin ƙarfafa ƙwarewa, ladabi da inganci a cikin aikin tsaro.
A cewar wata sanarwa daga hukumar DSS, wannan mataki na daga cikin kokarinta na tabbatar da bin ƙa’idodi na ɗabi’a da kuma inganta yadda ake gudanar da ayyukan tsaro.
Hukumar ta kuma bayyana cewa, an sallami jami’an ne bayan cikakken bincike da tantancewa a cikin shirin gyaran da ake gudanarwa.
DSS ta tabbatar wa ’yan Najeriya da kudirinta na ci gaba da kare tsaron ƙasa tare da gudanar da aikinta cikin gaskiya da amana.



