Wednesday, June 3, 2026
27.2 C
Bauchi

MUTUWAR WATA YARINYA A BORNO SAKAMAKON AUREN DOLE TA JANYO CECE-KUCE

MUTUWAR WATA YARINYA A BORNO SAKAMAKON AUREN DOLE TA JANYO CECE-KUCE

Wani mummunan lamari ya faru a karamar hukumar Gubio ta jihar Borno, inda wata matashiya ta kashe kanta bayan da mahaifinta ya dage sai ta auri abokinsa, duk da cewa ta nuna ba ta yarda ba.

Rahotanni daga yankin sun ce lamarin ya faru ne da yammacin Lahadi, misalin ƙarfe 6:20 na yamma, bayan matsin lamba da damuwar da ta dade tana fuskanta daga iyayenta domin tilasta mata wannan aure.

Wani mai sa ido kan kare hakkin yara a yankin Gubio, Bukar Fantami Gubio, ya tabbatar da faruwar al’amarin, yana mai cewa wannan lamari abin takaici ne kuma nuna yadda wasu mata ke fama da tauye ‘yancinsu a harkar aure.

A cewar Bukar Gubio, marigayiyar tun kafin rasuwarta ta sha bayyana cewa ba ta son auren mutumin da aka zaɓa mata, domin tana da wanda take so kuma take son aura. Duk da haka, iyalinta sun nace kan cewa dole ne a daura auren.

Ya ce tsananin damuwar zuciya da matsin da ta fuskanta daga iyali da al’umma shi ne ya sanya ta daukar wannan matakin na kashe kanta, yana mai kiran lamarin a matsayin abin da za a iya kaucewa da an mutunta ‘yancinta.

Mr. Gubio ya yi kira ga kungiyoyin kare hakkin dan Adam, hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki da su binciki lamarin cikin gaggawa tare da tabbatar da an samu adalci, domin zama izina ga makamantan irin wannan aiki.

Haka kuma ya roki iyaye, masu kula da tarbiyya da shugabannin al’umma su daina tilasta ‘ya’ya mata aure ba tare da yardarsu ba, yana mai jaddada cewa hakan na karya ‘yancin dan Adam kuma cin mutunci ne ga mata.

A halin yanzu, rundunar ‘yan sandan jihar Borno da gwamnatin jihar ba su fitar da wata sanarwa ba kan lamarin, yayinda al’ummar Gubio ke ci gaba da nuna alhini da mamakin aukuwar wannan abu mai raɗaɗi.

Related Articles

Popular Categories