Thursday, June 4, 2026
25.3 C
Bauchi

Hatsarin Mota a Yobe: Mutum Shida Sun Rasu, Takwas Sun Jikkata

Suleiman Isa

 

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Yobe ta tabbatar da mutuwar mutum shida, tare da jikkatar wasu takwas, sakamakon mummunan hatsarin mota da ya faru a ranar 17 ga Oktoba, 2025, da misalin ƙarfe 3:00 na rana, a kan babbar hanyar Potiskum zuwa Fika, kusa da Maiduwa Junction.

Mai magana da yawun rundunar, SP Dungus Abdulkarim, shi ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a ranar Asabar.

A cewar sanarwar, motar Sharon mai lamba PKM 549 YZ, wadda Adamu Hassan ke tukawa daga Potiskum zuwa #Bajoga a ƙaramar hukumar Funakaye ta Jihar Gombe, ta yi hatsari bayan direban ya rasa kulawar mota saboda gudun wuce sa’a.

Sanarwar ta ce, “Sakamakon hatsarin, fasinjoji shida sun mutu a nan take, yayin da wasu takwas suka samu munanan raunika.”

Jami’an Sashen Harkokin Motoci na Fika sun isa wurin da hatsarin ya faru cikin gaggawa, inda suka kai waɗanda suka jikkata da gawarwakin mamatan zuwa Asibitin Gwamnati na Fika, kuma likita ya tabbatar da mutuwar mutum shida.

A halin yanzu, ana ci gaba da ƙoƙarin gano iyalan mamatan domin tantance su da karɓar gawarwakin.

Rundunar ‘yan sandan ta danganta faruwar lamarin da gudun wuce ƙa’ida, tuƙi cikin ganganci, yin ƙoƙarin wucewa ba tare da izini ba, da kuma sha ko amfani da miyagun ƙwayoyi daga wasu direbobi.

Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Yobe, CP Emmanuel Ado, ya mika sakon ta’aziyya ga iyalan mamatan, tare da yi wa waɗanda suka jikkata fatan samun sauƙi cikin gaggawa.

Ya kuma yi kira ga direbobi da masu amfani da hanya da su rika bin ƙa’idojin zirga-zirga, su guji duk wani hali da zai jefa rayuka cikin haɗari, yana mai gargadin cewa masu tuƙi cikin ganganci za su fuskanci hukunci mai tsanani.

Rundunar ta kuma bukaci haɗin kai tsakanin ’Yan Sanda, Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa (FRSC), Kungiyar Direbobi ta NURTW, da sauran hukumomi domin ƙara wayar da kai kan muhimmancin kula da motoci, tuƙi cikin natsuwa, da nisantar amfani da miyagun ƙwayoyi.

Haka zalika, an kirayi jama’a da su rika kai rahoton duk wani direba da ke tuƙi cikin hatsari ko masu tuƙi cikin maye, ta layukan gaggawa na rundunar domin ɗaukar mataki cikin lokaci.

Sanarwar ta ƙare da cewa: “Muna iya kare rayuka idan muka hada kai domin tabbatar da tsaro da kiyaye dokokin hanya.”

Related Articles

Popular Categories