Sunday, April 19, 2026
39.1 C
Bauchi

Nuna Adalci da Hadin Kai: Gwamnan Bauchi Ya Raba Kayan Kirsimeti na ₦540m ga Kiristoci

Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya amince da ware kudin Naira miliyan dari biyar da arba’in (₦540m) domin saye da raba kayan abinci da na amfani ga al’ummar Kirista a Jihar Bauchi, domin su yi bikin tunawa da haihuwar Annabi Isa Almasihu (Yesu Kristi), wanda ake yi a duk shekara ranar 25 ga Disamba.

Shugaban Kwamitin rabon kyaututtukan Kirsimeti, Mr Abdon-Dala Gin, ne ya bayyana hakan yayin rabon kayan ga wadanda suka ci gajiyar shirin a Jihar Bauchi, Arewa Maso Gabashin Najeriya.

 

Mr Abdon-Dala Gin ya ce, tun bayan hawansa mulki a shekarar 2019, gwamnatin Gwamna Bala Mohammed ta dauki wannan a matsayin al’ada ta nuna kulawa da al’ummar Kirista, musamman a lokutan bukukuwa, tare da ba da muhimmanci ga Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) reshen Jihar Bauchi.

Ya bayyana cewa kayayyakin da aka amince da rabawa daga cikin kudin sun hada da bijimai 171, raguna 222, buhunan shinkafa 3,462, da kuma jarkokin man gyada 504 masu lita 25-25.

 

A cewarsa, za a raba kayayyakin ga rukunonin CAN guda biyar, jam’iyyun siyasa a jihar, ma’aikatan gwamnati Kiristoci, da sauran masu cin gajiyar shirin, ciki har da mutanen da ke da bukatu na musamman, a matsayin nuna kauna, hadin kai da zaman lafiya.

 

Ya kara da cewa, Gwamna Bala Mohammed ya kuma amince da sakin albashin watan Disamba ga ma’aikatan gwamnati da masu mukaman siyasa, domin su samu damar yin siyayyar bukukuwan Kirsimeti na bana.

Kwamitin, a madadin daukacin al’ummar Kirista a Jihar Bauchi, sun nuna godiya ta musamman ga Gwamna Bala Mohammed bisa kyautatawa, gaskiya da shugabanci na kowa da kowa, tare da jaddada cewa wannan tsari ya kawar da bambancin ra’ayi, sannan suka yi alkawarin cikakken goyon baya da hadin kai domin nasarar gwamnatinsa.

Related Articles

Popular Categories