Sunday, April 19, 2026
37.2 C
Bauchi

SHUGABA TINUBU YA UMURCI A JANYO ’YAN SANDA DAGA VIPs, A MAYAR DA SU KAN AIKIN TSARO NA GASKIYA

 

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin gaggawa na janye dukkan ’yan sanda da aka tura wa manyan mutane (VIPs) a faɗin ƙasar nan, tare da umartar a mayar da su kan aikinsu na asali domin ƙarfafa tsaro a ƙasa.

 

Wannan umarni ya biyo bayan wani muhimmin taron tsaro da Shugaban Ƙasa ya gudanar a ranar Lahadi a Abuja tare da shugabannin rundunar ’yan sanda, sojojin ƙasa, sojojin sama da hukumar DSS.

 

A cewar wata sanarwa da Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Yada Labarai da Tsare-Tsare, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Lahadi, tsarin sabon umarnin ya tanadi cewa masu buƙatar jami’an tsaro daga cikin VIPs za su rika samun rakiyar jami’an Civil Defence (NSCDC) maimakon ’yan sanda.

 

Fadar Shugaban Ƙasa ta ce matakin wani ɓangare ne na ƙoƙarin ƙara yawan jami’an ’yan sanda a cikin al’umma, musamman a yankunan karkara inda rashin isassun jami’ai ya hana samun tsaro da saurin daukar mataki.

 

Domin ƙara ƙarfin ma’aikata, Shugaba Tinubu ya riga ya amince da daukar karin ’yan sanda 30,000. Haka kuma Gwamnatin Tarayya na aiki tare da gwamnatocin jihohi domin inganta cibiyoyin horas da ’yan sanda a faɗin ƙasar.

 

Taron na ranar Lahadi ya samu halartar Shugaban Sojojin Ƙasa, Laftanar Janar Waidi Shaibu; Shugaban Sojojin Sama, Air Marshal Sunday Kelvin Aneke; Sufeton Ɗan Sanda na Ƙasa, Kayode Egbetokun; da Darakta-Janar na DSS, Tosin Adeola Ajayi.

Related Articles

Popular Categories