Sunday, April 19, 2026
37.2 C
Bauchi

HARE-HAREN DAJI A BAUCHI: ’YAN SANDA BIYAR SUN RASU A FARMAKI A DARAZO

 

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi ta tabbatar da rasuwar jami’anta guda biyar, yayin da wasu biyu suka jikkata, sakamakon farmakin da wasu ’yan bindiga suka kai wa tawagar ’yan sanda a kauyen Sabon Sara da ke Karamar Hukumar Darazo ta jihar.

A cikin wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar, CSP Ahmed Wakili, ya fitar, ya ce lamarin ya faru ne a ranar 22 ga Nuwamba, 2025, misalin ƙarfe 12:40 na rana, bayan da haɗaɗɗiyar tawagar jami’an ’yan sanda ta fita aikin sintiri bisa bayanan sirri domin dakile rikicin manoma da makiyaya a yankin.

Tawagar ta haɗa da jami’an Rapid Response Squad, Mobile Police 10 PMF Bauchi, Anti-Kidnapping Unit da kuma State Intelligence Department, inda aka yi musu kwanton ɓauna ta hannun wasu matasan da ba a tantance ba.

Harin ya yi sanadiyyar mutuwar jami’an ’yan sanda biyar kamar haka:

DSP Ahmad Muhammad – Sashen Bincike na Musamman (SID)

ASP Mustapha Muhammad – PMF 10

Inspector Amarhel Yunusa – PMF 10

Inspector Idris Ahmed – PMF 10

Corporal Isah Muazu – Anti-Kidnapping Unit

Haka kuma jami’ai biyu sun jikkata, su ne:

Inspector Isah Musa – SID

Inspector Yusuf Gambo – SID

Bayan faruwar lamarin, Divisional Police Officer na Darazo, SP Auwalu Ilu, ya jagoranci ƙarin tawagar jami’ai zuwa wurin don ceto waɗanda suka jikkata da kuma ɗaukar gawarwakin waɗanda suka rasu zuwa Asibitin Gabaɗaya ta Darazo.

Rundunar ta bayyana cewa an kashe wani adadi da ba a bayyana ba daga cikin maharan a musayar wuta, kuma ana cigaba da bincike domin kamo sauran waɗanda suka tsere.

Kakakin rundunar ya ce, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, CP Sani-Omolori Aliyu, ya ziyarci wurin don tantance halin da ake ciki tare da jajanta wa iyalan jami’an da suka rasa rayukansu.

Ya kuma tabbatar wa jama’a cewa rundunar za ta ci gaba da jajircewa wajen kamo masu laifin da suka aikata wannan ta’addanci, tare da tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi a faɗin jihar.

Related Articles

Popular Categories