Kungiyar Malaman Jami’o’i ta ƙasa, wato ASUU, ta sanar da dakatar da yajin aikin gargadi na makonni biyu da ta fara a ranar 13 ga Oktoba, 2025.
Shugaban ASUU na ƙasa, Farfesa Chris Piwuna, ya bayyana hakan a taron manema labarai da aka gudanar a Abuja da safiyar yau Laraba, 22 ga Oktoba. Ya ce an ɗauki wannan mataki ne bayan gwamnatin tarayya ta sabunta alkawuran da ta ɗauka na warware muhimman matsalolin da ƙungiyar ta gabatar.
Dakatarwar ta zo ne bayan kwana guda da shugaban Kungiyar kwadago (NLC), Joe Ajaero, ya gana da duka ƙungiyoyin ilimi, inda ya bai wa gwamnati karin makonni huɗu don kammala tattaunawa, tare da jan hankali kan cewa idan gwamnati ta nace da “No Work, No Pay”, to su ma za su rungumi “No Pay, No Work”.
Doka ta 43, sashe na 1(a) na Trade Dispute Act ta ƙasa tana bayyana cewa, “Duk ma’aikacin da ya shiga yajin aiki ba shi da haƙƙin karɓar albashi ko wani hakkinsa a lokacin yajin.”
A cewar Farfesa Piwuna, da ba a shiga wannan yajin aiki ba da farko, da ace gwamnati ta nuna gaskiya da cika alkawari tun farkon tattaunawar.
ASUU ta fara wannan yajin ne bayan karewar wa’adin gargadi na kwanaki 14, tana zargin gwamnati da sakaci da yarjejeniyar 2009 tsakaninta da ASUU.
Muhimman bukatun kungiyar sun haɗa da:
– Biyan albashin da aka tsaida,
– Bashin karin girma (promotion arrears),
– Kudin aikin koyarwa da bincike (Earned Academic Allowances),
– Fitar da kudaden third-party deductions,
– Da kuma kudaden farfaɗo da jami’o’in gwamnati.
Da wannan cigaba, ɗalibai a fadin ƙasar za su fara samun sauƙin rai yayin da zaman karatu ke dab da dawowa. Ku ci gaba da kasancewa tare da mu a Duniya Voice TV don karin bayani.



