Wednesday, June 3, 2026
27.2 C
Bauchi

Janar Markus Yake (Rtd) ya zama Gung-Zaar na farko na Sarautar Zaar a Jihar Bauchi

DA DUMI-DUMI

 

Brigadier Janar Markus Yake (mai ritaya) ya bayyana a matsayin wanda ya lashe zaben neman sarautar Gung-Zaar na farko na al’ummar Zaar, bayan takarar da ta gudana cikin kwanciyar hankali amma cike da gasa tsakanin ’yan takara.

 

Sarautar Gung-Zaar ita ce sabuwar madafun iko da za ta wakilci al’ummar Zaar da sauran ƙananan kabilu da ke cikin kananan hukumomin Bogoro da Tafawa Balewa a Jihar Bauchi.

 

A cewar sanarwar Ma’aikatar Hukumomin Kananan Gwamnati da Masarautu, wacce Jami’ar Yaɗa Labarai na ma’aikatar, Khadija Kobi, ta sanya wa hannu, an karɓi takardun neman wannan sarauta daga ’yan takara bakwai, sannan aka tantance su gaba ɗaya bisa ka’idar Dokar Sarauta ta Jihar Bauchi ta 2025.

Sanarwar ta ce zaben ya biyo bayan wallafa sanarwar buɗe damar ga masu sha’awar sarautar domin gabatar da takardunsu. Sai dai daga cikin ’yan takara bakwai, uku sun janye kafin zaben, lamarin da ya bar mutum huɗu da suka fafata a zagaye na ƙarshe.

 

A ƙarshe, Brigadier Janar Markus Yake (mai ritaya) ne ya samu nasara, kuma za a miƙa sunansa ga Gwamnan Jihar Bauchi domin amincewa da shi tare da naɗa shi a hukumance a matsayin Gung-Zaar na farko na Sarautar Zaar, da ke Bauchi ta Kudu, Arewa Maso Gabashin Najeriya.

 

Related Articles

Popular Categories